Mamakon ruwan sama ya shanye gidaje da dama a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba a safiyar ranar Litinin.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da kogin Mayo Gwoi ya malalo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka dauki tsawon sa’o’i biyu ana tafkawa.
Gidajen da ambaliyar ta shafa suna kusa da gabar kogin.
Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, amma ambaliyar ta lalata dukiya da suka hada da kayan gida da kuma kayayyakin abinci na miliyoyin Naira.
Ruwan saman dai kusan shi ne na farko-farko tun bayan da daminar bana ta fadi a yankunan Arewa.