Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i a Najeriya (JAMB) ta ce masu rubuta jarrabawar kimanin 60,000 ne suka gamu da matsaloli a cikin kwana biyun da suka wuce.
Adadin wani kaso ne a cikin mutum 947,000 da suka rubuta jarrabawar JAMB a wannan lokaci.
Shugaba sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana haka bayan rangadin wuraren da ake rubuta jarrabawar tare da Babban Magatakardan hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede da sauran jami’ai ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce an sake sanya ɗaliban lokacin da su je su rubuta jarrabawar tasu.
Ya ba da tabbacin cewa za a bai wa duk wanda ya yi rijista don rubuta jarrabawar JAMB dama yin hakan, yana cewa hukumar ta shawo kan matsalolin na’urorin da aka fuskanta a ranar farko ta rubuta jarrabawar a wasu cibiyoyi da ke faɗin ƙasar.
Dr Fabian Benjamin ya ce wannan ce jarrabawa mafi inganci da suka taɓa yi a tsawon shekaru, ko da yake ya san wasu za su yi jayayya da abin da ya faɗa saboda matsalolin da aka samu ranar Talata.