- Yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da aka cimma a Sudan – tsakanin ɓangarorin da ke faɗa wato sojojin ƙasar da kuma dakarun RSF za ta kawo karshe a daren yau. Ana ci gaba da faɗa a sassan ƙasar duk da cimma yarjejeniyar.
- Ma’aikatar lafiya a Sudan ta ce akalla mutum 512 ne aka kashe a rikicin kawo yanzu, tun baya ɓarkewar faɗa a rabar 15 ga watan Afrilu. Sai dai ana tunanin cewa alkaluman za su iya fin haka.
- Kusan ƴan Birtaniya 536 aka kwashe daga Sudan. BBC ta tattauna da mutane da ke isa filin jirgin Larnaca da ke Cyprus.
- Sakataren harkokin wajen Birtaniya James Celeverly ya bai wa ƴan ƙasar da ke Sudan shawarar cewa su fice nan take.Ya ce babu tabbacin cewa za a iya ci gaba da aikin kwashe mutane bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta.
- BBC ta samu rahotanni da ke cewa mayaƙa na ci gaba da addabar fararen hula a birnin Nyalain a kudancin yankin Darfur, abu kuma da ke nuna cewa rikcin ya yaɗu zuwa wajen Khartoum, babban birnin ƙasar.
- Motocin bas ɗauke da wasu daga cikin ɗaliban Najeriya ya tashi daga Sudan a jiya Laraba, inda ya nufi ƙasar Masar.
- Haka nan ma sauran ƙasashe da dama na ci gaba da kokarin kwashe ƴan ƙasarsu da ke Sudan a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta ta kwanaki uku ke kawo karshe.