An sa sunan Pelé gwarzon ɗan ƙwallon duniya a Dikshinari

0
78

Laƙabin Pelé, da ake faɗa wa marigayi gwarzon ɗan ƙwallon duniya, bisa ƙa’ida ya shiga cikin ƙamus, inda yake nufin “zaƙaƙuri ko fintinkau ko abu na daban”.

Ƙamusun harshen Fotugal (Portuguese) mai suna Michaelis, ɗaya daga cikin mafi shahara a Brazil, ya sa sunan “pelé” a matsayin sabuwar kalmar siffa a kundinsa na intanet.

Sanya sunan a cikin ƙamusu, ya zo ne bayan wani gangami da Gidauniyar Pele ta ƙaddamar na neman a karrama tauraron ɗan ƙwallon, inda ya samu amincewa har mutane fiye da 125,000 suka sa hannu.

Pele dai ya mutu a watan Disamban bara yana da shekara 82.

Shi kaɗai ne ɗan ƙwallon da ya ci Kofin Duniya sau uku, kuma mutane da yawa na ɗaukar sa a matsayin ɗan ƙwallon ƙafa mafi fice a tarihi.

A lokacin sana’arsa ta ƙwallon ƙafa tsawon shekara 20, ya ci ƙwallayen masu yawa a tarihi har 1,281 lokacin da ya buga wa ƙungiyar Santos ta Brazil da kuma a ƙasar Brazil da kulob ɗin Cosmos na New York.

Tun rasuwarsa, sanadin larurorin da ya yi fama da su na cutar dajin hanji, tsohon kulob ɗinsa Santos da tashar wasanni ta SporTV da Gidauniyar Pelé suka yi ta matsa lamba don ganin an martaba sunan tauraron ƙwallon ƙafan na duniya, ta hanyar shigar da shi cikin ƙamus.

A ranar Laraba ne kuma, masu buga ƙamusun Michaelis suka sanar da cewa za a shigar da kalmar cikin kundin kalmominsu na intanet a nan take.

Kuma da zarar an zo wallafa kwafen takarda na ƙamus Michaelis nan gaba za a haɗa da kalmar pele.

An sanya sunan kamar haka: “pe.lé adj. (siffa) Mutum wanda ya zarce saura, wanda nagartarsa, ƙima ko fifikonsa ba ɗaya ne da komai ko da kowa ba, kamar dai Pelé, laƙabin Edson Arantes do Nascimento (1940-2022), wanda ake ɗauka a matsayin ɗan wasa mafi gawurta a tsawon dukkan zamani kuma zaƙaƙuri, mai fintinkau kuma na-daban.”

Gidauniyar Pelé, wadda ƙungiyar agaji ce da aka kafa don alkinta tarihin gwarzon ɗan ƙwallon, ta ce karramawa ce da ta dace ga “sarki”.

“Kalmar da tuni ake amfani da ita wajen bayyana mutumin da ya yi fice kan abin da yake yi, ta shiga shafukan ƙamus!,” ta wallafa a saƙon tuwita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here