Gwamnatin tarayya ta tsawaita wa’adin janye tallafin man fetur

0
115

Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar tsawaita wa’adin cire tallafin man fetur har bayan wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari a kujerar mulki.

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a wannan Alhamis din yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

A cewarta, Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa NEC ce ta yanke shawarar cewa ba yanzu ne lokacin da ya dace a cire tallafin man fetur ba a kasar.

Ministar wadda ta bayyana hakan bayan kammala zaman majalisar wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta, ta ce dole ne a sake nazari tare da taka-tsan-tsan dangane da radadin da ’yan Najeriya za su fuskanta sanadiyyar janye tallafin man.

 

Ta ce a yanzu shirye-shiryen da tuni sun yi nisa za su ci gaba da gudana musamman ta fannin tuntubar dukkanin masu ruwa da tsaki ciki har da wakilan sabuwar gwamnatin Zababben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Zainab ta ce “Majalisar ta amince da cewa dole ne a cire tallafi na farko cikin gaggawa ba tare da wani ɓata lokaci ba, domin kuwa ba abu ne mai ɗorewa ba.

“Ba za mu iya ci gaba da biya ba. Dole mu kalli yadda cire tallafin ba zai jefa rayuwar ‘yan Najeriya ba cikin mawuyacin hali.

“Akwai buƙatar neman mafita bayan cire tallafin muna buƙatar yin shiri game da hakan domin tabbatar da an taimaka wa mutane da cire tallafin zai shafa.”

Gwamnatin Najeriya ta ce ta karɓo aron dalar Amurka miliyan 800 daga Bankin Duniya domin sassauta wa mutane raɗaɗin cire tallafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here