Kofin gasar Premier ya koma hannun Manchester City – Guardiola

0
124

A daren ranar Laraba ne dai ‘yan wasan City suka lallasa takwarorinsu na Arsenal da kwallaye 4-1 a filin wasa na Ettihad.

A lokacin da yake tsokaci bayan wasan da suka fatata, Guardiola ya kara da cewar, a halin yanzu kofin gasar Premier na hannun Manchester City

Nasarar dai ta bai wa kungiyar damar rage tazarar da ke tsakaninta da Arsenal zuwa maki biyu kacal, yayin da kuma take da kwantan wasanni biyu da za ta buga, abinda  ke nufin kungiyar na da ragowar  wasanni 7, kafin a karkare gasar Premier ta bana.

A halin yanzu Manchester City na da damarmakin lashe kofuna uku a kakar wasa  ta bana, da suka hada da na FA, na Premier da kuma na gasar Zakarun Turai, wadda z ata kara da Real Madrid a wasan kusa da na karshe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here