‘Sanadin fyaɗe aka haife ni – amma ba zan bari ya lalata min rayuwa ba’

0
116

Akan samu cikin yara da yawa ta hanyar yi wa iyayensu fyade, kuma in ji gwamnati akan iya gane waɗannan yara cikin sauƙi a Ingila da Wales.

A irin waɗannan ƙasashe, mutanen da aka yi wa iyayensu mata fyaɗe suka haife su, kan bayar da labarin yadda abin ya faru – su kuma yi bayanin yadda suka ƙi yarda hakan ya daƙile burikansu.

Zuwa ga Tas,

Kwananki 10 da haihuwa, amma lokacin da za ki karanta wannan wataƙila kin girma.

Ina matuƙar ƙaunarki.

A karon farko da Tasnim take karanta wasiƙar mahaifiyarta Lucy, sai da idanunta suka cika da hawaye. Ba ta san da wasiƙar ba, kuma ba ta san yadda wuta ta kashe mahaifiyarta Lucy ba, lokacin tana jaririya.

Wani tabon ƙuna ne a kumatun Tasnim kaɗai alamar da ke nuna abin da ya faru a wancan daren.

Yayin da wutar ta fara cin gidan, sai mahaifin Tasnim ya ɗauke ta zuwa wani wuri mai aminci, ya nannaɗe ta da wani bargo ya ajiye ta kusa da bishiyar tuffa a wani lambu.

Ya ceci rayuwarta – amma kuma shi ne ya zuba fetur ya kuma cinna wuta, wadda ta yi sanadin mutuwar ‘yar uwar mahaifiyar Tasnim da kakarta.

Tasnim ta san cewa an tabbatar da mahaifinta ya yi kisan kai, kuma yana zaman ɗaurin rai da rai ne a gidan yari.

Amma wasiƙar da aka manta a hannun ‘yan sanda sama da shekara 18, har sai da Tasnim ta nemi a fito mata da takardun shari’ar mahaifiyarta ta gani aka ganta – tana ɗauke da wani mummunan labari mai rikitarwa.

Yayin da Tasnim ta karanta, sai lamura suka dagule mata, saboda ta gano an same ta ne ta hanyar cin zarafin fyaɗe da mahaifinta ya yi wa mahaifiyarta.

Akwai fata da burikan da Lucy ta so ta cimma a rayuwarta, amma a gefen wasiƙar ta yi bayanin yadda ta sha wuya cikin sirri.

Mahaifin Tasnim ya raine ta tare da riƙa cin zarafinta tun tana shekara 12, direban motar tasi ne Azhar Ali Mehmood, kuma ya girmi Lucy da shekara 10.

Wannan lamari ya bar Tasnim cikin ɗimuwa. Ji take babu wanda ya shiga irin wannan yanayin a duniya kamarta. Sai dai bincike na nuna akwai irinta birjik.

Da wuya a iya cewa ga adadin mutanen da aka haifa ta hanyar fyaɗe da cin zarafi a Burtaniya, sai dai wani hasashen haɗin gwiwa da jami’ar Durham da cibiyar nema wa mata adalci suka yi, ya ce akwai mata 3300 da aka yi wa ciki sakamakon fyaɗe a Ingila da Wales a 2021 kaɗai.

Ƙudurin da za a kawo a Ingila da Wales zai riƙa ɗaukar yaran da aka haifa dalilin fyaɗe a matsayin waɗanda aka yi wa laifi.

Hakan in ji ministoci, zai tabbatar musu da damar samun ɗauki – ciki har da tuntuɓar ƙwararru da samun bayanai kan shari’arsu.

An kuma yi musu alƙawarin samun dama wajen kula da lafiyarsu idan suna fama da shan barasa da jarabar shan kwaya, za a ba su irin wannan dama a ɓan garen ilimi da samun gidaje.

Ba tare da samar musu irin wannan taimakaon ba yara kamar Tasnim za su kasance cikin wani yanayi na ruɗani ba tare da samun taimakon kwararru ba.

“Kana ta tunanin yayenka sun rayu cikin harin ciki da soyayya,” a cewarta.

“Ya sauya duk wani abu da kasani, da yadda kake kallon rayuwa kan iyayenka da kuma kai kanka.

Amma saboda ina da alaka da wanda ya aikata kisan kai kuma ya yi fyaɗe nakan ji muggan tunani irin na abin da ya aikata wani lokacin, Yanzu ina amfanin na girma na kwaikwayi abin da ya yi?”

Wani ɓangare na wasiƙar ya yi wa Tasnim tsauri ba za ta iya karanta shi ba. Tana ta ƙoƙarin ganin yadda za ta mayar da hanakali kan ɓangaren da ya shafi soyayyar da Lucy ta rubuta mata. Wasiƙar cike take da waƙoƙi da labaran inama sun yi rayuwa tare.

“Ba na jin haushin kai na, saboda mahaifiyata ba ta so hakan ba,” in ji Tasnim.

Neil ya yi wani ya yi wani gauron numfashi kan ya buɗe takardar wasiƙar.

Ya tashi a matsayin ɗan da aka raina ba tare da iyaye ba – a yankin West Yorkshire – Neil wanda ya ce ce ya yi rayuwa cikin farin ciki – kuma ko da yaushe na son jin abin da ya shafi mahaifiyarsa.

Sun san ya buri irin na sarauniyar almara da ke fatan wata rana za su sake haɗu.

Yanzu da yake da shekara 27, Ya buɗe wasiƙar da wani mai bincike mai zaman kansa ya samo daga gareta.

Da suke karantawa sai ya ji tamkar yana silalowa ne daga wani tsauni.

Wani baƙo ne ya yi wa mahaifiyar Neil fyaɗe a wani wajen shaƙatawa lokacin tana ƙarama. Sakamakon haka aka haife shi.

“Ba wani shiri da ka isa ka yi wa irin waɗannan kalaman,” in ji Neil.

Jin an tabbatar da cewa an kama su da aikata irin waɗannan laifuka, masu karya zuciya sai ka ji ” kamar wani ya daki ƙirjinka ya fasa shi”.

Ya ƙara da cewa “Kullum kana cikin jin kunya, da damuwa, ka rasa inda za ka dosa. Ba abin da za ka riƙa ji sai damuwa da tashin hankali a kanka. Ji nake na gama rushewa.”

Ka san abin da aka haife ka cikin tashin hankali yake nufi maimakon soyayya? Mahaifiyar Neil ta taɓa fatan ta ga sun haɗu?

Tasnim na jin kamar zuciyarta na bugawa za ta fito daga ƙirjinta lokacin da ta ji an rufe ƙofar gidan yarin da take bayanta.

Mai gadin wajen ya raka ta wani ɗan ƙaramin ɗaki mai sanyi, akwai kujeru biyu da teburi guda na jiran waɗanda za su zauna a kansu.

Sai aka buɗe wata ƙofa daga gefe sannan Tasnim ta ga mahaifinta karon farko. Sanye da kayan fursunoni ruwan toka, bai kai tsawon da take zato ba.

Ya rungume ta. ya kawo mata alawa,” cikin farin ciki.

Ba wannan Tasmin ke buƙata ba. So ta yi ta zama ita ta yi komai. So ta yi ta fahimtar da shi illar abin da ya aikata.

Yanzu da idanunta ta ga mutumin da ya cuci mahaifiyarta.

Tasnim ta fice daga gidan yarin ba kuma ta sake komawa ba. Ta samu amsar da take nema.

Ta koma jira a bakin tashar jirgin ƙasa domin haɗuwa da mahaifiyarsu a karon farko, cikin Neil na ta kaɗawa saboda fargaba.

Sun yi ta tunanin wannan lokacin da kuma gwada yadda za su haɗu da ita da abin da za su ce mata.

Tana fitowa Neil ya san ita ce.

Su biyun suka kalli juna. Beil ya ji duk ya ƙagu.

“Idan na ga yi kama da mutumin da ya maki haka, zan ta fi na bar nan,” in ji Neil.

” Ba ka yi ba, in ji mahaifiyarsu, Neil ya ji kamar an sauke masa wani nauyi a kafadarsa.

Mahaifiyar da ɗanta sun tafi suna tattaunawa, a nutse suna bai wa junansu labarin rayuwarsu.

Ta yi magana kan ‘yan uwansu, shi kuma Neil bai san komai a kai ba. Su biyu suna abubuwa irin ɗaya, har dariyarsu.

Neil bai tambayi abin da ya faru ba a wannan daren da aka tabbatar musu da laifinsu.

Ba sa son su san komai akan kuma ba sa son su mayar mata da hannun agogo baya.

Neil shi ji yake ba shi da mahaifi. Uwa ce da shi kaɗai kuma ta ishe shi.

Ga Neil da Tasnim, sauyin rayuwar da suka samu sun yarda cewa ya taimaka a ji koken mutane masu makamancin yanayinsu.

Suna fatan magantuwar da suka yi, za ta sanya wasu da aka yi cikinsu ta hanyar fyaɗe su zo su maganta.

“Akwai nuna kyama kwarai, wanda bai kamata ba,” in ji Tasnim.

“Ba maganar waye ya haifeka ake ba, maganar wane ne ni ake yi. kuma ba laifina ba ne. Wannan abu ya shafe ni.”

Yadda take tattauna maganar mahaifiyarta da mutane shi ke sanya ta jin daɗi. Ta yi imanin cewa ba haka labarin rayuwarsu ya kamata ya zama ba.

“Idan har ta kama na yi magana da mahaifiyata, dole na faɗa mata ƙimar da take da ita a zuciyata,” in ji Tasnim.

“Kuma in faɗa mata cewa komai na tafiya daidai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here