‘Yan sanda sun kama ‘yan daba 83 a lokacin bukukuwan sallah a Kano

0
132

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ce ta yi nasarar kama ‘yan daba 83 a lokutan bukukuwan karamar Sallah da aka yi a makon da ya wuce.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar a ranar Laraba, ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce kamen masu laifin ya taimaka wajen gudanar da bukukuwan Sallar lafiya.

“An kama ‘yan daba 83 daga tsakanin ranar Juma’a 21 ga Afrilu da ta kama Sallah zuwa Talata 25 ga Afrilu a lokutan Hawan Daushe da Hawan Nassarawa da Hawan Dorayi a fadin masarautu biyar na jihar,” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa “An kama masu laifin da mugayen makamai da miyagun kwayoyi da kuma kayayyakin sata a hannunsu.”

A yanzu haka ana binciken masu laifin, in ji rundunar ‘yan sandan.

Sanarwar ta ce an yi wannan aiki ne karkashin umarnin da Babban Sufeton ‘yan sandan kasar Usman Alkali Baba ya bayar na tabbatar da samar da tsaro a lokutan hidimomin sallah.

Kazalika sanarwar ta gode wa sauran hukumomin tsaro da kungiyoyin fararen hula da sarakuna da ‘yan sa kai da sauran masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen dakile aikata miyagun laifuka a lokutan hidimar.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta jaddada aniyarta ta tabbatar da tsaron al’ummar Jihar Kano, tare da gargadin masu aikata laifi da kuma jan hankalin mutane da su ci gaba da yi wa jihar addu’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here