An gano gawarwakin wadanda suka mutu da yunwa don kwadayin shiga Aljanna a Kenya

0
103

Adadin wadanda zama da yunwa sakamakon umarnin shugaban wata kungiyar addinin Kiristanci a Kenya ya kai mutum 98, inda ‘yan uwa da abokan mambobin kungiyar suke cikin kuka da alhinin da jiran samun labarai game da jama’arsu.

Gano gawarwaki da dama da aka binne a dajin Shakahola na kusa da garin Malindi na kan gabar teku ya girgiza jama’ar Kenya, inda ake zargin shugaban kungiyar Paul Mackenzie Nthenge da yaudarar mabiyansa kan cewa ta hanyar zama da yunwa ne kadai za su shiga Aljanna.

Wannan mummunan al’amari da aka kira shi da “Kisan Kiyashin Dajin Shakahola” ya janyo kiraye-kirayen murkushe kungiyoyin addini na bogi a kasar, wadda mabiya addinin Kirista suka fi yawa.

“Mun fuskanci kalubale da dama yau saboda ruwan sama, amma a karshe mun ciro gawarwaki takwas”, in ji wani jami’in dan sanda a yayin zantawa da AFP, wanda hakan ya kawo adadin wadanda aka gano sun mutu a lamarin zuwa 98.

Jami’an sun bayyana cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukan.

“Nthenge ya fada wa mabiyansa su zauna da yunwa don tunkarar karewar duniya a ranar 15 ga Afrilu, kuma shi ne zai zama na karshe a saboda haka zai kulle kofa,” kamar yadda Stephen Mwiti wanda matarsa da ‘ya’yansa shida ne suka shiga kungiyar, kuma ana zaton duk sun mutu.

Mwiti ya bayyana cewar ya samu wannan bayani ne daga wani mamba na kungiyar wanda aka kora saboda ya sha ruwa a lokacin da ake zama da yunwa.

Jami’an asibitin garin Malindi na gabar teku da ake kai gawarwaki da wadanda suka tsira sun ce sun ji irin wadannan labarai daga bakunan wadanda suka tsira da rayukansu.

“Nthenge ya yaudari mabiyansa manya da mata da matasa da yara kanana da cewar shi ne zai zama mutum na karshe da zai hana kansa abinci har ya mutu.”

Mwiti ya kai korafi wajen ‘yan sanda, amma kuma an ki a saurare shi. Kakakin ‘yan sandan yankin ta bayyana cewa daga baya za ta amsa tambayar tofa albarkacin bakinta kan lamarin da aka yi.

Iyalai da dama sun dimauce a wajen ajiye gawarwaki na asibitin Malindi inda suke sauraren ko an gano ‘yan uwansu.

Mahaifiyar Issa Ali ce ta kai shi Shakahola a shekarar 2020 kuma ya shaida wa AFP cewar ya sha dukan kawo wuka a wajen Nthenge a lokacin da ya so ya bar wajen sa, har sai da mahaifinsa ya kubutar da shi.

Yaron mai shekara 16 ya ce “A karo na karshe da na ga mahaifiyata shi ne a watan Fabrairu”

“Ta jigata sosai a lokacin da na gan ta a karon karshe”

Hassan Musa dan kasar Kenya kuma jami’in kungiyar Red Cross ya shaida wa AFP cewa mutum 311 da suka hada da yara 150 ne aka bayar da rahoton sun bata a Malindi.

Ya ce “Muna magana ne game da mutanen da suke ‘yan kasar Kenya, akwai wasu daga Tanzaniya da Nijeriya. Wasu sun bata tsawon shekaru.”

Abun damuwa ne yadda ake samun coci-coci suna koma wa wasu kungiyoyin kamar na asiri a Kenya, inda shugabanninsu suke koyar da tsaurin ra’ayi da ke jefa rayuwar mabiya a cikin fitina.

Mafi yawan wadanda abun ya shafa yara ne kanana

“Ba mu san kaburbura nawa, ko mutane nawa za mu sake ganowa ba,” in ji MInistan Harkokin Cikin Gida Kithure Kindiki a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce wannan laifi ne babba da zai sanya a iya tuhumar Nthenge da aikata mummunan laifi.

Mafi yawan wadanda suka mutu yara ne kanana. Kamar yadda wasu majiyoyi uku da suka yi bincike suka sanar, inda suka bayyana irin akidun kungiyar da ke kiran iyaye su bar ‘ya’yansu da yunwa.

Hussaini Khalid, Daraktan Zartarwa na Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta ‘The Haki Africa” wanda suka tseguntawa ‘yan sanda abun da Nthenge yake yi, ya shaida wa AFP cewar fasto na fara bukatar yara su fara zama da yunwa, sai mata, sannan kuma maza manya.

Ya ce, kashi 50 zuwa 60 wadanda lamarin ya shafa yara ne kanana da aka samu gawarwakinsu a nannade a fararen kyalle a ckinin ramuka marasa zurfi.

Malaman coci bata-gari

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya yi alkawarin daukar matakan ba sani ba sabo kan malaman coci bata-gari irin su Nthenge ”wadanda ke amfani da addini wajen dabbaka ra’yoyin da ba za a amince da su ba.

A lokacin da ake ci gaba da bincike, ana ta mamakin ta yaya har wannan kungiya ta ci gaba da aiki bayan an kai shekara shida da ‘yan sanda suka san irin abubuwan da yake yi.

An tama kama mutumin a 2017 bisa zargin koyar da tsattsauran ra’ayi inda yake kira ga iyaye da kar su tura yaransu makarantun boko saboda a Bible babu inda aka ce a yi boko.

A watan da ya gabata ma an sake kama Nthenge bayan wasu yara kanana biyu sun mutu a hannun ‘ya’yansu saboda hana su abinci.

An sake shi bayan biyan belin dala 700, kuma a ranar 2 ga watan Mayu aka tsayar da ranar da zai gurfana a gaban kuliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here