Dalibar jami’ar Yobe ta yanke jiki ta mutu bayan zana jarabawa

0
136

Wata dalibar jami’ar jihar Yobe (YSU), da ke garin Damaturu, Maryam Lawan Goroma, ta kwashi jiki ta fadi inda rai ya ce ga garinku bayan ta kammala zana jarabawa.

LEADERSHIP ta tattaro cewa dalibar ta yanki jiki ta fadi ne a ranar Alhamis 27 ga watan Afrilun 2023 kuma an garzaya da ita zuwa asibiti ruwa-ruwa amma likita ya tabbatar da mutuwarta.

Abokin karatunta, Mallam Bukar Maisandari, shi ne ya tabbatar da batun mutuwar, inda ya ce, ita Maryam din lafiyarta kalau kafin ta fadi ta mutu.

“Innaa Lillaahi Wa Innaa Ilaihir Raaji’uun. Cikin alhini da jimami nake samun labarin rasuwar abokiyar karatunmu, Maryam Lawan Goroma.

“Cikin koshin lafiyarta take kafin ranar yau (Alhamis) lokacin da ta kwashi jiki ta fadi kuma aka tabbatar da mutuwarta ‘yan dakika kalilan. Muna addu’ar Allah ya jikanta ya gafarta mata kura-kuranta, ya kuma sanyata cikin aljanna madaukakiya.

“Ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalanta da ‘yan uwanta, abokai, kawaye da abokan karatunta a sashin darasin Chemical. Allah ba ku hakurin jure wannan rashi,” ya rubuta.

An yi mata jana’iza a ranar Juma’a kamar yadda addinin musulunci ya shimfida a gidansu da ke Sabon Fegi da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here