Ganduje na yi wa shirin miƙa mulki zagon ƙasa – NNPP

0
105
Ganduje
Ganduje

Jam’iyyar NNPP mai jiran gado a Kano ta zargi gwamnatin jihar mai barin gado da yin zagon ƙasa ga shirin miƙa mulki hannun sabuwar gwamnati.

A wani taron manema labarai a ranar Juma’a, shugaban kwamitin miƙa mulki na gwamna a jam’iyyar NNPP Dr Abdullahi Baffa Bichi ya yi zargin cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, da gangan tana kawo cikan ga shirin miƙa mulki.

Ya ce gwamnatin ta bai wa jam’iyyar NNPP gurbi uku kawai a cikin kwamitin da aka kafa don miƙa mulki hannun sabuwar gwamnati.

Bayan zaɓen 18 ga watan Mairis ne aka bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano, inda ya kayar da ɗan takarar jam’iyya mai ci ta APC a ƙarkashin gwamna Abdullahi Ganduje.

Dr Baffa Bichi ya ce “mutanen jihar Kano sun cancanci samun shirin miƙa mulki da zai tafi salin alin ba tare da tangarɗa ba.”

Ya ce ba su amince da tsarin da gwamnatin ta gabatar musu na cewa ɓangarenta ne zai kawo kashi 82 na ‘yan kwamitin miƙa mulki hannun sabuwar gwamnati ba.

Sai dai har zuwa yanzu ba a ji wani abu daga gwamnati mai barin gado ba, kan zargin da jam’iiya mai jiran gado ta yi a kanta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here