Akalla dalibai 88 ne da ke fama da nakasar gani a ranar Alhamis suka zana jarabawar gama-gari a Kano.
An gudanar da atisayen ne a cibiyar Jami’ar Bayero Kano (BUK).
JEOG wani shiri ne da aka tsara don ba da dama ga masu fama da nakasa musamman makanta don rubuta jarabawar kyauta.
An bai wa daliban maza da mata na’urori daban-daban kamar na’urorin hannu, na’urar rubutu, da takardan makalawa don saukaka ayyukan jarabawar.
Ko’odinetan JAMB na cibiyar Kano, Farfesa Yahuza Bello ne, ya bayyana haka a lokacin da yake sa ido kan aikin da aka gudanar a Makarantar Ci gaba da Ilimi ta BUK.
A cewarsa, mutane 337 da ke fama da makanta ne suka yi rajista domin zana jarabawar a cibiyoyi 11 na kasar nan.
“Wannan kokari na ci gaba ne na JAMB karkashin Farfesa Oleyede, don tabbatar da cewa babu wani dan Nijeriya da ya cancanta da za a hana shi damar yin jarabawar UTME da samun ilimi mai zurfi ba tare da la’akari da nakasa ba.
“Tun da aka kafa ta a shekarar 2017, JEOG ta tantance dalibai sama da 3,300, inda sama da kashi uku suka amince da kwasa-kwasan da suka zaba a manyan makarantun Nijeriya,” in ji Bello.