Mutanen Kaduna sun koka kan matsalar wutar lantarki

0
243

Mazauna Jihar Kaduna sun koka kan matsalar rashin wutar lantarki da ke ci musu tuwo a kwarya, musamman a wannan yanayin da ake fama da zafi.

A yanzu haka unguwanni irinsu Tudun Wada da Hayin Malam Bello da Unguwar Sanusi da Nariya da Rigasa da kuma Sabon Gari da suka kwashe kwanaki babu wutar lantarki.

A wasu lokuta kuma idan aka kawo wutar ba ta wuce ’yan mintuna sai a dauke, wanda hakan ya sa unguwanni da yawa ke fama da rashin ruwan sha.

Aminiya ta lura da cewa a Tudun Wada a kullum magidanta musamman mata da ’ya’yansu na gararambar neman ruwan sha saboda yancinsu da wutar ake janyo ruran rijiyayn burtsatse.

Wani mazaunin unguwar Hanyin Bello, wanda kuma yake sana’a a Tudun Ilu da ke yankin Tudun Wada, Samaila Shittu ya bayyana wa Aminiya damuwarsa a kan rashin wutar.

“Kwanakinmu kusan hudu ke nan babu labarin wutar lantarki, babu kuma wata magana mai dadi daga Hukumar wutar Lantarki ta jihar.

“Dubi yadda mutane ke wahala wajen neman ruwan Sha,” inji shi.

Shi mawani mazaunin Unguwar Nariya, wanda aka di sani da Alhaji Bayerabe kira ya Yi da kamfanin rarraba wutar da su raba wa gidaje mita mai amfani da kati da zai baiwa mutane damar sayan wutar da suke Sha.

“Tsarin kawo wa mutane takardun kudin wuta duk wata ba adalci ba ne.

“Mutane na kyashin biyan ne saboda ba su aha wutar ba.

“Su raba wa gidaje mita kowa ya rika sayen iya wutar da zai sha a duk wata,” inji shi.

Da aka tuntubi Jami’in Hulda da jama’a na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jihar, Abdul’azeez Abdullahi,  ya dora alhakin rashin wutar a kan rashin samun isasshiyar wuta daga Babban tashar Samar da wuta ta kasa watau ( national grid).

Ya ce a ’yan kwanaki baya kusan megawatts 149 (MW) aka ba su su rabawa jihohin Kaduna da Sakkwato da Zamfara da Kebbi wanda kuma ya Yi kadan matuka.

A saboda wannan dalilai ne ya sa dole ake karba-karba da wutar a tsakanin unguwanni, a cewarsa.

“Sannan batun samun isasshen wuta ya danganta ne da yadda ake biyan kudi a-kai-a-kai domin amfana da shi.

“Idan kwastamomi suka ki biyan kudinsu ko suka biya kadan-kadan ko suka ki biya gaba daya, hakan na shafar samun wuta.

“Don haka akwai bukatar Kwastamomi su dauki alhakin biyan kudin wuta domin samun ingantacciyar wutar lantarki.

“Muna fama da bashi da ke hannun kwastamominmu. Hakan ya sa muka yanke kwastamomi da ba su biya,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here