Nijeriya ta fara biyan ma’aikata albashin da aka yi karin kashi 40 cikin 100

0
84

Gwamnatin Nijeriya ta fara biyan mai’aikata albashin da aka yi musu karin albashi da kaso 40 cikin 100.

Sai dai kuma wadansu ma’aikatan na gwamnatin tarayya da ke karkashin wasu tsare-tsare na daban, ba za su ci moriyar wannan karin albashi ba, ciki har da Malaman jami’o’i da sojoji da ma’aikatan lafiya, kasancewar ba sa karkashin tsarin biyan albashi na bai daya.

Karin albashin ya shafi ma’aikatan da ke karkashin tsarin biyan albashi na bai daya su dubu 144,766, kuma karin zai kai har kan alawus-alawus dinsu.

Tabbacin haka ya samu ne a wata wasika da hukumar kula da biyan albashin kasar ta fitar karkashin jagorancin Ekpo, inda wasikar ta ce iyakacin ma’aikata 144,766 ne za su ci moriyar wannan ci gaba.

Amma sai dai wannan sako bai yi wa kungiyar Malamai ta ASUU dadi ba, ganin yadda aka cire su cikin wadanda za su mori wannan ci gaba na karin albashi har kaso 40 cikin dari.

Kungiyar Malaman Jami’ar tana mai cewa ba ta ga dalilin da zai sanya a cire ta daga cikin wadanda za’a karawa yawan albashi ba, duk da cewa su ma an yi musu kari a baya-bayan nan.

Shugaban kungiyar na kasa Farfesa Emmanuel Osedeke ya ce kungiyar za ta nazarci wannan batu, kuma za ta sanar da matakin da za ta dauka da ya dace.

A watan da ya gabata ne Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi na kasar, Dakta Chris Ngige ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da karin albashin ma’aikatan gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here