Saudiyya ta gindaya sharuɗɗan fita da Zamzam daga ƙasar

0
106

Hukumomin filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke birnin Jidda a Saudiyya sun sanya sharua hudu ga duk wnda ya yi ziyara yake so ya tafi ƙasarsa da ruwan Zamzam.

Cikin wata taswirar bayanani game da masu ibadar da za su koma ƙasashensu da aka fitar, an haramtawa masu ɗaukar robar ruwan Zamzam a cikin kayansu, sai dai su riƙe shi a hannu a cikin jirgi.

Masu gudanar da ayyukan sun sanar da cewa ko wanene ke son siyan Zamzam sai dai ya siya daga ainihin waɗanda ke siyarwa a wuraren tsayawarsu, kuma lita biyar kawai aka yarda mutum ya ɗauka.

Ko wanne mai ibada ba zai ɗauki sama da roba guda ba ta ruwan Zamzam, kuma sai ya nuna shaidar rijistar umara ta manhajar Nusuk.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here