Yadda ‘dan fashi’ ya sa mace jefar da jariri a garin kwace mata waya a Kano

0
90

Wani matashi da ake zargi da fashi da makami ya bayyana yadda ya sa wata mata ta jefar da jaririnta sabuwar haihuwa ta gudu a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya.

Matashin ya firgita matar ne sakamakon bin ta da ya yi da wuka domin ya kwace mata waya wanda hakan ya sa ta jefar da jaririnta.

Wannan matashin dai yana daga cikin mutum 83 da rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta kama kan zargin aikata laifuka a lokacin bikin Karamar Sallah.

A wani bidiyo da mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ga matashin dan shekara 22 mai suna Ibrahim Muhammad yana bayani kan abin da ya yi.

“Wata mata ce ranar 1 ga Sallah suna tafiya na bi su da wuka na karbi waya, an ba ni wayar ma amma tsautsayi ya sa na sake bin su daga baya har ta jefar da jaririn,” kamar yadda matashin ya bayyana wa ‘yan sanda.

Ya kara da cewa bai kai ga caka mata wukar ba aka kama shi.

Ibrahim wanda ya ce shi mazaunin Unguwar Sabuwar Gandu ne, ya ce wannan ne karo na farko da ya yi irin wannan lamari kuma a cewarsa ba ya shaye-shaye.

Duk da matashin ya roki sassauci, amma rundunar ‘yan sandan Kano ta ce ba za a kyale matashin ba sakamakon zarginsa da yunkurin fashi da makami da kisan kai, abin da rundunar ta kira da ‘manyan laifuka’.

Rundunar ‘yan sandan ta ce a halin yanzu ana gudanar da bincike a kansa inda daga bisani za a gurfanar da shi a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here