‘Yan bindiga sun shimfida wa al’ummar yankin Birnin Gwari sharuddan noma a damunar bana

0
77

Duk da dosowar daminar bana, manoma a yankunan Birnin Gwari sun ce har yanzu sharar gona don shirin fara noma ya gagara saboda ‘yan bindiga da ke yankin sun shinfida sharudan da manoman ba za su iya cikawa ba.

Babban dajin Birnin Gwari da ya hada yankunan jihohi uku na Kaduna, Neja da Zamfara, yana daga cikin wuraren da ake noma kaso mafi tsoka na kayan abinci a yankin.

To sai dai tsawon shekaru ke nan manoma a yankin ba sa samun sukunin yin noma, sakamakon mamayar da ‘yan bindiga suka yi a wajen.

Hasali ma kauyuka da dama sun tashi daga yankin, saboda ayyukan ‘yan bindigar, da suka hada da kai hare-hare, satar shanu da kuma satar mutane domin karbar kudin fansa, wanda ya zama ruwan dare a yankin.

Yanzu haka ana tunkarar saukar damina, amma babu alamun wani shirye-shiryen soma kintsawa aikin gona a yankunan na dajin Birnin Gwari da kewaye kamar yadda aka al’adanta, na share gona, kai taki da dai sauransu.

Mai sharhi kan lamurran yau da kullum kuma Dan-masanin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Idris Abdurra’uf ya ce bana ma dai lamarin ya ta’azzara, saboda sharudda masu tsaurin gaske da ‘yan bindigar su ka shinfidawa manoma.

Ya ce ”yanzu dai aikin gona ya gagara a yankin Birnin Gwari duk kuwa da bukatar da manoman ke da ita na zuwa gona don soma shirye-shirye da hako arzikin albarkatun noma a yankin.

Wannan matsala dai ta dade tana ci wa mahukuntan Nijeriya tuwo a kwarya, kamar yadda kwamishinan tsaro na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana wa manema labarai, bayan tashi daga wani taro kan sha’anin tsaro a Kaduna, inda ya ce duk da nasarorin da jami’an tsaro ke samu kan ‘yan bindiga, har yanzu akwai kalubalen tsaro.
To sai dai duk da ta’azzarar wannan matsalar ta tsaro, Dan masanin Birnin Gwari, na ganin akwai mafita idan aka sauya salo.

Ya ce “sai an yi da gaske. Jami’an tsaro suna iya kokarinsu. Amma maganar nan da nake da kai, tsakanin Manina da Mariga ‘yan bindiga na cin karensu ba babbaka. Kullum suna harbe na harbewa, su raunata wasu, sannan su kwashi wasu mutane a shiga da su daji domin karbar kudin fansa.”

“Saboda haka dole jami’an tsaro su sauya salo kuma su kara kaimi, sannan a sami wadanda za su taimaka musu a shiga cikin wadannan dazukan, domin duk abin da aka yi kan hanya idan ba’a shiga dazukan ba, to ba yadda za’a yi a kawo karshen wannan matsala.”

Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan-bindiga ke shinfida wa manoma sharudan zuwa gonakin su ba, sai dai kuma manazarta na ganin saka ka’idojin tun kafin sharar gona alama ce ta sauya salon da ke bukatar mahukunta su dauki mataki tun kafin abin ya gagari kundila.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here