An kashe hatsabibin dan ta’adda yayin da ya je garkuwa da dan kasuwa a Katsina

0
98

’Yan sanda sun halla wasu ’yan bindiga biyu ciki har da daya daga cikin wadanda suka kai hari a makaranar GSS Malumfashi da ke jihar Katsina a shekarar 2020.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, Gambo Isah ya ce sun aika ’yan ta’ddan lahira ne a lokacin da suka yi kokarin sace wani dan kasuwa a garin Katsina.

Ya ce sun dakile ’yan ta’addar ne ta hanyar bibiyar tattaunawarsu ta waya, kuma sun kwace bindigogi kirar AK-47 guda biyu bayan kashe ’yan bindigar a musayawar wuta da suka yi ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa daga cikin ’yan ta’addan da aka kashe har da wani “Sama’ila Shehu, wanda takadarin dan bindiga ne da aka taba kamawa a shekarar 2020 kan harin da aka kai gidajen malamaan GSS Malumfashi aka kuma garfanar da shi a kotu a lokacin”.

Gambo Isah wanda ya ce rundunarsu tana ci gaba da bincike kafin ta fito da cikakken rahoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here