Matakin da kamfanin da ke dakon wutar lantarki a Nijeriya TCN ya dauka na saka takunkumi kan kamfanonin rarraba lantarki na Kaduna da Kano ya soma jefa jama’ar yankunan cikin wani hali.
A ranar Juma’a ne kamfanin na TCN ya sanar da dakatar da tura wa kamfanonin KAEDCO da KEDCO wutar lantarki.
Haka kuma TCN din ya saka takunkumi har kan kamfanin APLE.
Kamfanin na TCN ya ce ya dauki wannan matakin ne sakamakon saba wasu ka’idoji na kasuwanci da ya ce kamfanonin sun yi.
Kamfanin KEDCO dai yana rarraba wutar lantarki ne a jihohin Kano da Katsina da kuma Jigawa, sai kuma kamfanin KAEDCO yana rarraba wuta a jihohin Kaduna da Sokoto da Kebbi da Zamfara.
Ibrahim Dankanjiba wanda ke sana’ar dinki a Jihar Kaduna ya shaida wa TRT Afrika cewa tun kafin TCN ta dauki wannan mataki dama suna kwana su wuni ba tare da wutar lantarki ba, inda ya ce a yanzu wannan matakin zai kara musu kunci.
“Yanzu misali kamar ni ina sana’ar dinki, amma haka muke kwana mu wuni ba a samun wuta, ko da sun kawo ta ba ta wuce sa’o’i biyu zuwa uku,” in ji Ibrahim.
Jazuli Lawan wanda ke da shagon sayar da kayan motoci a Kantin Kwari a Jihar Kano ya shaida wa TRT Afrika cewa tun da aka dauke musu wuta a ranar Juma’a har zuwa Asabar ba a dawo da ita ba.
“Tun daga azumi zuwa yanzu wuta ta lalace, wannan azumin mun sha wahala sosai, wuta ce minti talatin awa daya a yini, idan mun samu kenan, wani lokacin sai mu kwana biyu uku ba wuta.
“Wannan matsalar sai dai mu ce Innalillahi wa inna ilaihi raji’una,” in ji Jazuli.
Shi kuwa Shu’aibu Abubakar wanda ke da shagon siyar da kayayyaki a unguwar Badarawa/Kwaru a Kaduna ya bayyana cewa sun kusan mako uku ba su da tsayayyar wutar lantarki.
“Mun kusan mako uku sai a kawo wuta a dauke amma yanzu tun da ta dauke kusan kwana shida kenan ba mu da ita ko kyal ba mu gani.
“Muna sayar da lemu da ruwa masu sanyi, gaskiya kasuwarmu ta dan samu nakasu sosai tsakani ga Allah,” kamar yadda Shu’aibu ya shaida wa TRT Afrika.
Ya bukaci gwamnati ta taimaka musu ta sa baki kan wannan lamari inda ya ce suna shiga wani hali.
Matsalar wutar lantarki na daga cikin matsalolin da aka dade ana fama da su a Nijeriya.
Gwamnatoci da dama sun sha alkawarin magance matsalar amma lamarin ya gagara.