’Yan ta’adda da suka yi garkuwa da yara sama da 85 a Jihar Zamfara sun sako 70 daga cikin yaran, amma sun kashe biyu.
A ranar Juma’a ’yan ta’addan suka sako yaran, kimanin mako uku bayan sun sace su daga kauyen Wanzamai na Karamar Hukumar Tsafe ta jihar.
Wani mazaunin yankin Sani Aliyu ya ce, “Yara biyu da ’yan bindigar suka kashe sun yi kokarin tserewa ne, wadanda aka sako din kuma sun galabaita saboda tsananin yunwa, kuma yanzu ana duba lafiyarsu.”
Ya ce ganin irin galabaitan da yaran suka yi ya sa iyayensu koke-koke, kuma “An sako su ne bayan an biya kudin fansa Naira miliyan shida; da farko miliyan uku aka ba su, amma suka ki sako su, sai an kara musu da sabbin babura guda biyu.”
Sai ya bayyana cewa duk da haka, akwai karin wasu yaran a hannun ’yan ta’addan, “ba mu san dalilin da suka ki sako su ba.”
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bangaren Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, amma hakarsa ta yin magana da kakakin rundunar, CSP Muhammad Shehu, ba ta cim ma ruwa ba.
Kimanin makonni uku da suka gabata ne ’yan bindiga suka ritsa wasu yara da suka je neman icen girki da wasu manya a gonaki suka yi awon gaba da su a yankin Tsafe na Jihar Zamfara.
Daga cikin manyan da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su har da mata.