Kamfanin samar da ruwa na kasar Ghana GWCL ya ce sakamakon soma ruwan sama, zai bude madatsar ruwa ta Weija domin rage adadin ruwan da ke ciki.
Hukumar watsa labarai ta kasar Ghana ta ruwaito kamfanin yana gargadi ga jama’ar da ke zaune a gefen madatsar ruwan da su yi kaura daga wurin domin gudun abin da ka je ka dawo.
Al’ummomin da ake fargabar idan an saki wannan ruwa za su iya samun ambaliya sun hada Tetegu da Oblogo da Pambros Salt da Lower McCarthy Hill.
Sauran kuwa sun hada da Lower Weija da Bojo Beach da Adakope da kuma al’ummomin da ke zagaye da wurin.
Kamfanin ruwan ya bayyana cewa matakin ruwan a ranar Juma’a 28 ga watan Afrilu ya kai kafa 46.
Hakan na nufin matakin ruwan a halin yanzu saura kafa daya ya kai kafa 4, wanda shi ne mataki makura da ba a so madatsar ruwan ta wuce.
Kamfanin ruwan na Ghana ya bayyana cewa duk bayan sa’a daya ake duba matakin ruwan da ke a madatsar kuma ya jaddada cewa ba zai yi shakkar bude madatsar ba idan ya ga matakin ya kai 46.5 domin kauce wa faruwar duk wata matsala.
Jama’a da dama sun rasa muhallansu a yankin da madatsar ruwan take sakamakon sakin ruwan da aka yi a Oktobar bara.
Haka kuma hukumar watsa labarai ta Ghana ta ruwaito shugaban hukumar kare afkuwar bala’i na kasar Eric Nana Agyemang Prempeh, yana cewa duka gidajen da aka gina a kan hanyar ruwa duk za a rushe su da zarar ambaliyar ruwan ta janye.