Gyara a dokar aikin Hajji zai rage tsadar tafiya Makkah a Najeriya – Sanata Dan Baba

1
201

Dan Majalisar Dattijai mai wakiltar Sokoto ta Kudu a Majalisar Dokokin Najeriya Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba ya sha alwashin yin duk abin da zai iya wajen ganin an yi wa dokar aikin Hajji kwaskwarima a sabuwar majalisa ta goma da za ta fara aiki.

Sanatan wanda ya kasance a tsohuwar majalisa ta tara wacce za ta gama aikinta cikin watan Mayun shekaran nan ta 2023 ya ce tun da farko ya gabatar da kudurin gyaran a gaban majalisar mai karewa.

Sanata Dan Baba ya kara da cewa lokaci ya yi da ya kamata a samar wa mahajjata sauki wajen biyan makudan kudade domin aikin Hajji.

A cewar dan majalisar, yin gyara ga dokar Hukumar Aikin Hajji ta kasar shi ne zai magance yadda ake samun karuwar kudin tafiya Hajjin.

Ya ce ya bukaci majalisa ta gudanar da bincike kan badakalar da ke cikin aikin Hajji a Najeriya kuma majalisar ta kafa wani kwamitin bincike.

“Biciken ya gano ana sama da fadi da kudaden mahajjata, otel da ya kamata a kama na kwana arba’in sai a kama na tsawon kwana casa’in sauran kwanakin kuma sai a sanya Larabawa a dakunan bayan alhazai sun tafi, sai a raba kudin tsakanin masu otel da kuma shugaban Hukumar Alhazai na wancan lokacin inda otel zai dauki kashi 25 shi kuma shugaba ya dauki kashi 75” A cewar Sanata Baba.

Dan majalisar ya ce kadan daga cikin kudaden da aka gano an wawure sun kai Naira biliyan daya.

Sanatan ya kara nuna bukatar yin kwaskwarima ga dokar wadda za ta hana duk wanda zai shugabanci hukumar ya yi abin da aka yi a baya.

Dan majalisar yana ganin Naira miliyan uku sun yi tsada ga masu zuwa aikin Hajji kuma da an dauki matakan da suka dace da kudin aikin Hajjin bai kai haka tsada ba a cewarsa.

Ya kuma kara da cewa lallai sai ya sake tayar da maganar a sabuwar majalisa har sai an bai wa mahajjata hakkinsu.

An shafe shekaru da dama ana kwan-gaba-kwan-baya kan batun yin gyara ga dokar a gaban majalisar dokokin ta Najeriya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here