RA’AYI: Aminu Dahiru, madubi ga matasan jahar Kano

0
98

Daga Hannatu Suleiman Abba

Duk da cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba, anma kuma ranar wanka ba a boyen cibi sanna yabon gwani ya zama dole.

A lokaci da dama nakan tuna yadda matasa suke gudun ‘yan uwansu matasa a bangaren ci gaban rayuwar su.

Hakan nada nasaba da yadda zuciyar dan Adam ke da rauni, amma duk da haka ana samun masu taimakon junan su ta bangarori da dama ,idan har damar tazo.

Idan zancen taimakawa matasa ake yi a jahar Kano idan aka zo wurin mataimaki na mussaman ga Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje a bangaren hoto, wato Aminu Dahiru Ahmad matashi ne kuma dan siyasa wanda ya zama abin kwatance ga duk masu kishi da ci gaban matasa a jahar Kano.

A kwananki baya, shaharren mai daukar hoto a jahar Abdulwahab Sai’d Ahmad Wanda aka fi sani da bluelens ya shirya taron horar da matasa Sana’ar daukar hoto.

Blue lense ya wallafa shirye shiryen hora da matasa a jahar shafin sa na fesbuk ,cikin ikon Allah da Aminu ya ga wanna sakon tuni ya bukaci zai dai nauyin su ba tare da bata lokaci ba.

Hakazalika, Ranar yaye daliban da suka samu horar daukar hoto ciki har da Mata da masu bukata ta mussaman, an samu hallatar mutane masu tarin yawa inda anan blue lense ya bude sabon ofishin sa na daukar hoto da jawabin Godiya.

A cikin jawabin blue lense a ranar taron yaye daliban,ya Kara bayyana cewa ba duk matashi da ya samu dama irin ta Aminu zai waiwayi ‘yan baya ba mussaman wadanda suke sana’a iri daya.

“Aminu ya kasance cikin wadanda suka bani gudumawa wajen bude wanna gurin, Kuma gudumawa mai tarin yawa.

“Hakazalika, wanna taron yaye daliban shi ya dau nauyi komai akan abun da za’a ci da kuma a sha, tare da bawa daliban kudin motar komawa gida.

“A matsayin na, na guda daga cikin shuwagabani masu daukar hoto a jahar Kano, tabbas bamu da abin cewa ga Aminu sai dai muyi masa sam barka. Saboda babu wanda bai amfana da abinda yake da shi ba ko babba ko karami, a zahiri ko badini, inji bluelens.

Yabonsa a bangaren taimako bai tsaya a gurin bluelens ba, haka yake a gurin saura masu Sana’ar daukar hoto kamar su Umar Faruk (shakaka), Muhammad Rabiu Naseer (tubeless ) da sauransu.

Ko a kwanakin baya, an gano wasu a shafin Facebook sun wallafa hoton sa akan yadda ya gyara wani masallaci da Al’ummar suka dade suna bukata.

Ko da aka same shi da zancen nan take ya isa gurin aka kuma fara aiki cikin ikon Allah.

Da watan Ramadan Haka yabi jama’a da rabon kayan abinci kuma bai bari an dau hoton sa lokacin da yake rabon ba kuma bai saka a shafin sa ba.

Idan muka dawo bangare siyasar sa, a cikin matasa yan siyasa da basa jam’iyya daya, babu wanda zai fadi aibun Aminu sai dai sam barka.

Cikin kwanciyar hankali zasu fadi irin taimakon da yake yi da kokarinsa na  kaucewa ba tare da an san waye ba.

Duk da cewa shi din matashi ne, haka bai hana shi duba marasa lafiya da Kuma inganta rayuwar masu bukata ta mussaman ba. Kamar yadda Zainab Nasser Ahmad take fada, Aminu Yana da saukin kai, son cigaban al’umma da kuma nuna kishin sa akan sana’a ga matasa.

“Alkhairin sa ba sai ya sanka ba ko kuma kana da alaka dashi ba, akwai wadanda matasa ne, sun fishi kuma sun samu mukami a matakin kasa amma har yau babu me gayamaka yadda al’umma ta amfana dasu” inji Zainab.

Wadannan kadan daga cikin abubuwan da nasani game dashi ne ta bangaren wayenda ya zauna dasu, sanna da bibiyar abokan siyasar sa.

Idan har matasa zasuyi koyi da Aminu to tabbas rayuwar gobe ta matasa ce. Ya samu shaida me kyau daga kowanne bangare a cikin rayuwa hakan na nuni da cewa, madubi ne Kai ga rayuwar yan baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here