Home Labarai Labaran Duniya Rikicin Sudan: Sama da mutane dubu 20 suka tsallaka zuwa Chadi

Rikicin Sudan: Sama da mutane dubu 20 suka tsallaka zuwa Chadi

0
106

Majalisar dinkin duniya ta ce akalla mutane dubu 20 ne suka tsallaka Sudan zuwa Chadi tun bayan barkewar  rikici tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun kai daukin gaggawa a farkon watan nan na Afrilu.

Darektan hukumar a Chadi, Pierre Honnorat na cewa bukatar ta yi tsanani sosai domin nan da makonni 6 ko 8 masu zuwa ba za su iya kai wa yankunan da masu gudun hijirar suke dauki ba saboda yanayi na ruwan sama.

Tun a farkon makon nan aka soma rabawa ‘yan gudun hijiran da suka isa kan iyakar Adre abinci da sauran kayakin jinkai.

Rikicin da aka shafe sama da makonni 2 ana yi ya mayar da Khartoum tamkar filin daga, sannan ya jefa illahirin Kasar cikin halin kaka-ni-kayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp