Tun a makon da ya gabata ne dai gwamnatin Najeriya ta shirya kwashe daliban zuwa kasar Masar dake makotaka da sudan din, don samun sauki wajen dawowa gida, toh saidai bayanai na nuna hukumomin Masar sun ki amincewa ‘yan Najeriyar su shiga kasarsu.
Ya zuwa yanzu ‘ya’yan Najeriyar da suka kaura daga babban birnin Khartum na Sudan tun a ranar laraba da ta gabata don isa Cairo kamar yadda hukumomin kasar suka tsara tun farko, na cigaba da kasancewa a makale a kan iyakar kasashen biyu.
Iyalan ‘yan Najeriyar da ke cigaba da kasancewa a Sudan sun shaidawa jaridar Daily Trust a daren ranar asabar cewa babu hikima a tsarin bin hanya guda wajen dawo da ‘yan Kasar gida.