An sake ceto daya daga cikin ‘yan matan Chibok bayan shekara 9

0
201

Sojojin Haɗin Gwiwa na Runduna ta 114 a Jihar Borno sun ceto ɗaya daga cikin ‘yan matan da aka sace a Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata da ke Chibok a ranar 14 ga Afrilun 2014.

Sunanta Hauwa Maltha kuma ita ce mai lamba ta biyu a cikin jerin ‘yan matan da aka sace.

Mai shekara 26 da haihuwa, an ceto ta ce a ranar 21 ga Afrilun 2023 tare da wata ‘yarta mai shekara 3 lokacin da sojoji suka farmaki yankin Lagara.

‘Yar ƙabilar Kibaku, an yi wa Hauwa auren dole da mai ɗaukar hoto na marigayi shugaban boko haram, Abubakar Shekau mai suna Salman a Gulusko wanda aka kashe a yankin Tafkin Chadi, daga bisani kuma aka sake aurar da ita ga wani Malam Muhammad a Gobara wanda shi kuma ta haifa masa ‘ya’ya biyu. Shi ma an kashe shi a wata gwabzawa da aka yi tsakanin ISWAP da Boko Haram a maɓuyar Ukuba.

An dai ceto Hauwa ce ɗauke da ciki wata takwas da sati biyu inda ake ta duba lafiyarta da ‘yarta mai suna Fatima. Ana shirin miƙa ta ga Gwamnatin Jihar Borno sakamakon sun wattsake.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here