Rikicin Sudan: An bude iyakar Masar ga ‘yan Najeriya bayan Buhari ya sa baki

0
123

An bude iyakar Masar ga ‘yan Nijeriya domin su wuce bayan Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sa baki, tare da taimakon Shugaban na Masar.

Shugabar hukumar da ke kula da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje Abike Dabiri ce ta bayyana haka inda ta ce an bude iyakar amma tare da sharuda masu tsauri.

Ta kuma bayyana cewa ba da jimawa ba ofishin jakadancin Nijeriya da ke Masar zai soma aikin kwasar ‘yan kasar.

Tun da safiyar Litinin gwamnatin Nijeriya ta koka kan cewa daliban Nijeriya da aka kwaso daga Sudan na nan makale kan iyakar Sudan din da Masar sakamakon kasar ta ki bude iyakarta ga daliban Nijeriyar su wuce.

Hukumar da ke kula da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje ce ta sanar da hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ce tuni jirgin saman Nijeriya samfarin C 130 ya isa filin jirgin Masar domin kwaso ‘yan kasar.

“Har yanzu iyakar Masar ba a bude ta ga dalibanmu ba, amma sojojin saman Nijeriya a shirye suke, jirgin NAF C 130 ya sauka a filin jirgin Aswan kuma sun ce [ba za mu tafi ba tare da dalibanmu ba],” in ji sakon da hukumar ta wallafa.

Ita kanta shugabar hukumar Abike Dabiri ta sanar da cewa jirgin ya je da tulin busashen abinci da magunguna da ruwan sha ga daliban.

Ranar Alhamis ne aka soma kwaso kashin farko na dalibai 1600 daga Sudan bayan sun kwashe kwanaki suna korafi game da mawuyacin halin da suka shiga sakamakon rikicin da ya barke a kasar tsakanin sojoji da dakarun runduna ta musamman ta Rapid Response Force, RSF.

Hukumar bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya, NEMA ta bayyana cewa tana sa rai daliban za su isa Abuja ranar Juma’a idan jirgin saman Air Peace ya kwaso su daga yankin Aswan na kasar Masar bayan sun isa can daga Khartoum.

Sai dai hakan bai yiwu ba sakamakon daliban sun kasa tsallaka iyakar ta Masar.

Tuni dama gwamnatin Nijeriyar ta sanar da cewa ‘yan kasashen waje kusan 7000, ciki har da ‘yan Nijeriya sun makale a Masar.

Gwamnatin Nijeriyar dai ta ce ofishin jakadancinta da ke Masar yana aiki tukuru don shawo kan matsalar a yayin da hukumomin Masar suka dage cewa sai kowanne dan Afirka ya samu biza kafin a bar shi ya tafi kasarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here