Ban yi nadamar sanar da Binani matsayin wacca ta ci zaben gwamna a Adamawa ba – Hudu Ari

0
120

A tattaunawar da shugaban INEC na jahar Adamawa Hudu Ari ya yi da manema labarai a yau Talata ya tabbatar da kalaman sa kan cewa bai yi nadamar ayyana Binani a matsayin wacca ta lashe zaben gwamnan jahar Adamawa ba.

Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ibrahim: Me za ka ce game da cewar da ake ka karbi kudi?

Hudu Ari: Ka karbi kudin mutum domin ka taimake shi ko dan ka yi masa wani abu haramun ne, babu wanda na karbi kudin sa a cikin su duka kawai dai zargi ne ina zan kai biliyan 2.

Ibrahim: To me ya sa ka bayyan Binani a matsayin wacca ta ci zaben bayan ba a gama tattara sakamakon zaben ba, kuma baka bayyana bayanan alkaluman da ta samu ba da kuma wanda sauran yan takara suka samu?

Hudu Ari: Ai an bayyana komai kawai takardar ce ba ta nan da na karanta maka,  Binani ta samu kuri’u 428,173, Fintiri  422,303.

Ibrahim: Yanzu ka yi nadamar abunda ya faru wanda ya jawo yan sanda ke neman ka  kake buya?

Hudu Ari: Ban yi nadama ba, kuma maganar buya ba buya nake ba zan je har ofishin su na amsa kira.

Ibrahim: Yaushe za ka je?

Hudu Ari: Sai na duba takardar da aka aiko min tukunna.

Ibrahim: Hukumar INEC ta ce ka zo ka yi bayanin yadda abun ya kasance amma ka ki zuwa?

Hudu Ari: Na rubuta musu takarda duk da ance ba su karba ba amma ni na san an karba.

Yadda tattaunawar ta kasance kenanan da shugaban INEC na jahar Adamawa Hudu Ari.

BBC News Hausa

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here