Mahara sun kashe mutum 2, sun sace 4 a Zariya

0
97

Wasu mahara da ake zargi ’yan fashin daji ne sun hallaka mutane biyu tare da sace wasu hudu a yankin Kofar Kona da ke garin Zariya.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, maharan da suka farmaki unguwar da misalin karfe 9.40 na daren ranar Litinin, sun kai kimanin mutane 50.

Wani mazaunin unguwar wanda ya bukaci a sakaya sunan shi, ya ce mayakan sun kai su hamsin kuma da isowar su suka zarce gidan wani jami’in Kwastam, Mallam Abubakar Modibbo.

A cewarsa, sun yi awon gaba da matarsa Asiya Abubakar da ’ya’yanshi mata guda biyu —Hafsat da Khadijatul Kubra.

Ya ce daga nan ne sai kuma suka yi awon gaba da wani magidanci mai suna Mallam Falalu Ibrahim.

“Bayan fitowar su daga gidan ne suka harbe mutane biyu, Zaharaddeen Mohammed da ke Amaru da kuma Sunusi Sani da ke Dorayi.

“Sai dai shi Sunusi Sani ya rasu ne da safe bayan an kai shi asibiti sakamakon rauni na harbin bindiga.

Wani dan kungiyar sa-kai wanda ya so a boye sunan shi, ya ce maharan bayan sun kammala da nan sun zarce kauyen Dorayi inda suka yi awon gaba da shanu masu yawa da kuma mutane sama da ashirin.

Sai dai ya ce sakamakon musayar wuta da suka yi da ’yan sintiri, ’yan fashin sun tsere sun kyale wadanda suka yi garkuwa da su.

Ya kara da cewa, a dalilin musayar wutar ce maharan suka kone gidan wani Alhaji Dalha tare da wasu babura guda biyu a unguwar ta Dorayi.

Duk kiran da wakilin mu ya yi ta wayar hannu domin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, amma hakan ya ci tura a dalilin rashin daukar wayarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here