Kotu ta bai wa EFCC damar karbe gidaje 324 a Kano

0
135

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, EFCC, ta ce wata kotu ta ba ta dama ta karbe gidaje 324 a Jihar Kano da ake zargi an gina ta hanyar amfani da kudaden haramun.

EFCC ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a soshiyal midiya ranar Laraba.

Ta ce Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya “ya bayar da umarni a karbe” gidajen kamar yadda EFCC ta bukata a wajensa.

Hukumar ta ce gidajen sun hada da guda 168 da ke Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Bandirawo City; guda 122 da ke Sheikh Nasiru Kabara (Amana City), Kano da kuma 38 da ke Sheikh Khalifa Ishaq Rabiu City, Kano.

EFCC ta kara da cewa gidajen sun hada da masu dakuna biyar-biyar, hurdudu, uku-uku da masu biyu-biyu da sauransu.

A cewarta, ana zargi an gina gidajen ne da “kudin da aka samu ta hanyar haramun daga hukumar Kula da ‘Yan Fansho ta Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here