Akwai yiwuwar maniyyatan Najeriya su kara kudin Hajjin bana

0
116

Akwai yiwuwar maniyata aikin Hajin bana daga Najeriya su biya karin kudaden kujerar tafiya sakamakon yakin da kae ci gaba da gwabzawa tsakanin sojoji da rundunar RSF a kasar

Bayanai sun ce kamfanonin jiragen saman da aka baiwa damar gudanar da jigilar ma’aikatan zuwa kasar Saudi Arabiya sun ki rattaba hannu akan takardun kwangilar da aka basu wanda aka shirya bikin gudanarwa yau alhamis.

Rahotan sun ce kamfanonin sun bukaci Karin lokaci domin sake nazari akan aikin da kuma duba sabbin hanyoyin da zasu bi domin kaucewa kasar Sudan da ake ci gaba da yaki.

Masana sun ce kaucewa sararin samaniyar Sudan zai kaiga tsawaita tafiyar da kuma biyan Karin kudade da kamfanonin jiragen za suyi saboda bi ta cikin kowacce kasa, wanda hakan ka iya kara farashin kujerar da aka riga aka biya.

Wannan ta sa aka dage bikin rattaba hannu akan kwangilar zuwa ranar Talata mai zuwa domin baiwa kamfanonin tantance yadda aikin zai gudana da kuma ko za’a samu karin kudi ko kuma a’a.

Kwamishinan kula da jigilar maniyatan a Hukumar alhazai ta Najeriya Abdullahi Hardawa ya tabbatar da dage rattaba hannu akan kwangilar zuwa makon gobe, amma bai yi bayani akan ko za’a samu karin kudin kujerar ba.

Sai dai masana sufurin jiragen sama sun tabbatar adcewar akwai yiwuwar samun Karin, wanda ake iya dorawa maniyatan ko kuma gwamnati lura da cewar kamfanonin na wannan aiki ne domin samun riba.

Kuma wannan matsala bata tsaya ga maniyatan Najeriya kawai ba, domin zata shafi duk wasu jiragen saman da suka saba bi ta sararin samaniyar Sudan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here