Matashi ya kashe mahaifiyarsa a Kano

0
96

Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta tabbatar da kisan wata mata mai suna Malama Jummai da wani matashin danta ya kashe ta da wuka a yammacin ranar Laraba.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, kakakin ‘yan sandan Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin kuma nan ba da jimawa ba za a yi cikakken bayani.

A daren da lamarin ya faru a birnin Kano ya shiga cikin rudani sakamakon rahotannin da ke cewa yaron mai suna Iro Kwarangwal da ke unguwar Karshen Kwalta a Rimin Kebe, ya daba wa mahaifiyarsa mai suna Jummai wuka har lahira.

Sai dai wani shaidan gani da ido, Muhammadu Abdu wanda kuma makwabcin marigayiyar ne, ya ce lamarin wanda ya faru jiya da misalin karfe 5:30 na yamma ya samo asali ne sakamakon rashin jituwa tsakanin mahaifiyar da yaron.

“Ina tsaye a wajen gidana, kwatsam na ji kururuwa.

“Bayan da muka garzaya domin kai taimako, mun iske marigayiyar wadda aka caka mata wuka da dama tana kururuwar neman taimako” in ji shi.

Ya kuma kara da cewa wanda ake zargin ya gudu daga wurin jim kadan bayan aikata danyen aikin ga mahaifiyarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here