Zargin Damfara: Kotu ta dage shari’ar A.A. Zaura

0
124

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta dage shari‘ar zargin tsohon dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na APC, Abdulkarim Abdussalam Zaura (A.A. Zaura) da aikata damafara ta Dala miliya 1.3m da Hukumar Yaki da Almundahana ta Kasa (EFCC) ta shigar gabanta.

Alkalin, Muhammad Nasir Yunusa ya dage zaman ne sakamakon rashin halartar shaidun masu gabatar da kara.

Tun da fari dai EFCC ta maka Zaura a kotu ne bisa zargin sa da damafarar wani dan kasuwa a kasar Kuwait a shekarar 2018 kudi Dala 1.3m.

A shekarar 2021 babbar kotun ta kori karar saboda rashin wadatacciyar shaida daga masu kara, amma kotun daukaka kara ta dawo da shari’ar.

Lauyan EFCC Sadiq Usaini ya roki kotun ta dage shari’ar, duk da bai bayyana dalilin kin zuwan shaidar tasa zaman ranar ba.

kotun dai ta dage zaman zuwa ranar 31 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni domin ci gaba da shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here