Akwai ‘yan Najeriya sama da miliyan 13 da ke da asusun banki ba su da BVN, in ji CBN

0
114

A Najeriya an yi hasashen cewa akwai kimanin mutum miliyan 200 na yawan ‘yan kasar, an bayyana cewa a cikin wadannan adadi akwai sama da mutum miliyan 70 da ke da asusun banki a bankunan kasuwancin Najeriya.

Cikin wadannan suke da asusun bankin, akwai ‘yan Nijeriya sama da miliyan 57 da ke da asusun banki kuma suna da lambar BVN, sai dai akwai sama da ‘yan Nijeriya 13 da suna amfani da asusun banki amma ba su da BVN.

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi hadin gwiwa da hukumar daidaita alaka a tsakanin bankunan Nijeriya (NIBSS) da kwamitin masu bankuna da kuma masu ajiya a bankuna domin kaddamar da aikin samar da lambar BVN a watan Fabrairun 2014.

An kirkiro lambar BVN ne ga masu mu’amula da bankunan Nijeriya domin tantance su wajen rage damfarar kudade da inganta gudanar da ayyukan bankuna a kasar.

Tun bayan bullo da lamarin, BVN ya kasance yana da matukar muhimmin wajen abubuwan da ake bukata don budewa da kuma kula da asusun banki a kasar nan.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka a birnin Kalaba wajen taron kara wa juna sani karo na 34 na masu aiko da rahotannin kudade da kuma editocin harkokin kasuwanci.

Emefiele wanda ya samu wakilcin Daraktan Sashen Kayyade Kudade na CBN, Dakta Hassan Mahmoud ya ce, “Har a zuwa ranar 31 ga Maris ta 2023, jimillar wadanda suke da BVN a Nijeriya guda 57,431,355, kuma BVN yana taimakawa wajen bunkasa harkokin ijiya a bankuna, wanda hakan zai taimaka don inganta damar samun rance ga masu karbar bashin bankuna.”

Gwamnan CBN ya kara da cewa BVN zai ci ci gaba da zama lambar tantance asusun banki da ke bukatar a matsayin wani bangare na shirye-shiryen saukaka wahalhalun da ke tattare da rashin tantance kwastomomin bankuna.

Ya ce CBN zai ci gaba da tallafa wa kwastomomin banki da ba su BVN domin su mallaki lambar ta saukakkiyar hanya.
Emefiele ya kara da cewa an gabatar da tsarin biyan kudi na PSB 2025 domin fadada hanyoyin biyan kudade ga abokan ciniki da kuma karfafa kula da tsarin biyan kudi.

Da yake karin haske game da tsarin biyan kudin, gwamnan CBN ya bayyana cewa babban bankin yana amfani da tsarin biyan kudi a matsayin wata hanyar samun nasara a harkokin kudade da kasar nan ta saka a gaba.

Bincike ya nuna cewa kashi 34 ne na ‘yan Nijeriya ke da asusun banki, kuma kashi 9 ne kacal ke iya gudanar da hada-hadar kudade ta hanyar fasahar zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here