An fara yi wa Aso Rock kwaskwarima gabanin rantsar da Tinubu

0
107

Yayin da ake shirin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayu, an fara yiwa fadar shugaban kasa da ke Aso Rock kwaskwarima, domin samar da kyakkywan sabon salon kala ga shugaba mai jiran gado.

Kwararrun ma’aikata da masu fanti sun dukafa da gyare-gyare da fantin bangwayen ginin fadar a kokarin shirye-shiryen mika mulki ga sabon shugaban.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram cewa a halin yanzu ana gyaran fadar shugaban kasa, Villa inda masu fanti ke ta famar aiki don ganin ta yi kyawun gani ga shugaba mai jiran gado.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here