Kane ya zama na biyu a yawan cin kwallaye a Premier League

0
95

Harry Kane ya zama na biyu a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Premier League a tarihi.

Tottenham ta doke Crystal Palace 1-0 a wasan mako na 35 a Premier League ranar Asabar, kuma Harry Kane ne ya ci kwallon.

Kane, mai shekara 29, kenan zura na 209 a raga a babbar gasar tamaula ta Ingila, kenan ya zarce tsohon dan wasan Manchester United, Wayne Rooney.

Tsohon dan wasan Newcastle United Alan Shearer shine kan gaba mai 260 a raga, yayin da Wayne Ronney ya koma na uku mai 208 a Premier League.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here