Za a fara ganawa kan rikicin Sudan a Saudiyya

0
95
Bangarorin da ke yakar juna a Sudan sun cika alkawarin fara zaman neman sasantawa a rigimar da ta haddasa asarar daruruwan fararen hula kawo yanzu.

Makonni uku bayan barkewar fada a Sudan, bangarorin da ke gaba da juna a kasar za su fara tattaunawa a Saudiyya da nufin duba yiwuwar tsagaita bude wuta.

Daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci zaman tattaunawar a wannan Asabar, har da mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro, Jake Sullivan.

Kafin yanzun ma dai an yi ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin tsagaita wutar tsakanin magoya bayan janarori biyu masu fada a Sudan din, wato da bangaren Mohammed Hamdan Daglo da Shugaba Abdel Fattah al-Burhan ba tare da an cimma nasara ba.

Sama da mutane 500 ne dai alkaluman gwamnati ke cewa suka salwanta a sabon rikicin na kasar Sudan, adadin da wasu kwararrun ke cewa zai fi haka ganin akwai wadanda suka mutu ba tare da an sani ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here