Alkawarin da Tinubu ya yi wa ma’aikatan gwamnati

0
105
Tinubu

Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ma’aikata tabba-cin samun kyakykyawan rayuwa a gwamnatinsa.

Ya ce zai ba su fiye da mafi karancin albashi da za su iya gudanar da rayuwarsu da ta iyalansu.

Ya kuma yi alkawarin zama amintaccen aminin ma’aikatan kasar nan da zaran an rantsar da gwamnatinsa a ranar 29 ga Mayun 2023.

Wadannan alkawuran na kunshe ne a cikin sakon bikin ranar ma’aikata na wan-nan shikerar da ya sanya wa hannu.

Da yake tabbatar wa ma’aikatan kasar nan ta hannun kungiyar kwadago (NLC) da kuma kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), Tinubu cewa “Da zarar an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu a matsayin shugaban Nijeriya, ma’aikata za su samu fiye da mafi karancin albashi. Za ku sami albashi fiye da mafi karancin albashi da za ku iya gudanar da rayuwarku da ta iyalanku.

“A karkashin shugabancina, za ku sami ‘yanci da walwalan aiki wajen yakir rashin adalci na zamantakewa da tattalin arziki ga daukacin ‘yan Nijeriya, gami da duk ma’aikata.

“Yakinku zai zama yakina, saboda a ko da yaushe ni zan muku yaki. Ina da shirye-shiryen inganta walwala da yanayin aiki mai kyau a cikin ajandar gwamnatina, saboda samar da ingantaccen Nijeriya.

Alkawari ne akai na tun lokacin da aka hai-fe nake kokarin yadda za a inganta rayuwar ma’aikata.”

Da yake kiran hadin kan ma’aikata, Tinubu ya shawarce su da cewa, “Kwanaki masu zuwa, ana bukatar fahimtar juna da hadin kai daga kowane bangare, saboda shugabanci na bukaci mu dauki tsauraren matakai domin jama’armu da ma’aikatan Nijeriya su samu rayuwa mai inganci.”

Zababben shugaban kasar ya nemi goyon daukacin ma’aikatan Nijeriya, inda ya nemi ma’aikata da su hada kai da gwamnatinsa mai jiran gado wajen yakir fatara, jahilci, cututtuka, rashin hadin kai, kabilanci da mambancin addini da duk wani mummunan lamari da ka iya barazana ga zaman lafiya da hadin kan kasa.

Tinubu ya yaba da irin rawar da ma’aikatan Nijeriya suke takawa wajen gina kasa.
Ya ce, “Na bi sahun sauran kasashen duniya da sauran ‘yan’uwa domin murnar ranar ma’aikata ta duniya ta bana. Yau rana ce ta musamman a mafi yawan kasashen duniya, rana ce ta gaisuwa da karrama ma’aikatan da kwazonsu da guminsu ke ci gaba da rura wutar ci gaban Bil’adama.

“Wannan rana tana da matukar mahimmanci ta fuskoki da yawa. Rana ce da aka kirkira saboda gwagwarmayar neman hakkin ma’aikata da ‘yancinsu na zaman-takewa da tattalin arziki. Tun daga shekara ta 1891, aka fara bikin wannan rana a duk fadin duniya.

“A Nijeriya, kowace ranar 1 ga Mayu rana ce ta musamman a kalandar kasarmu. Ranar hutu ce ga al’umma da muke yi ba wai don tunawa da gudunmawa da sa-daukarwar da ma’aikata suke bayarwa ba ne don ci gaban kasarmu ce.

Ta kasance ranar bikin hakkin ma’aikata da kare mutuncisu da ingantaccen albashi da rayuwa mai kyau, kuma mafi mahimmanci shi ne, muhimmiyar rawar da kungiyar kwadago ke takawa wajen hadin kan kasarmu.

“Tun a shekarar 1945 lokacin da ma’aikatan jirgin kasa da wasu kungiyoyin ma’aikatan gwamnati 16 suka jagoranci yajin aikin farko na neman karin albashi sakamakon tsadar rayuwa, kungiyar kwadago a Nijeriya a ko da yaushe tana yaki domin talakawan kasarmu.

Ba abin mamaki ba ne cewa kungiyar ta kara kuzari ga gwagwarmayar neman ‘yancin kai ta hanyar hada kai da masu kishin kasa irin su Nnamdi Azikiwe, Herbert Macaulay, Ahmadu Bello, Obafemi Awolowo, Ernest Ikoli da Anthony Enahoro da sauransu.

“Haka kuma an samu kungiyar kwadago a Nijeriya ne a daidai lokacin da muke gwagwarmayar maido da mulkin dimokuradiyya. Kungiyar kwadago ta Nijeriya da kungiyoyin da ke da alaka da ita kamar irin su NUPENG, Tedtile, PENGASSAN, da dai sauransu, sun hada kai da shugabanni da kungiyoyi masu fafutukar tabba-tar da dimokuradiyya wajen maido da mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a shekarar 1999 bayan kusan shekaru biyu na mulkin kama-karya na sojoji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here