Ba na kamun ƙafa don Tinubu ya naɗa ni shugaban ma’aikata-El-Rufai

0
112

Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya musanta jita-jitar da wasu ‘yan Najeriya ke yi cewa yana sha’awar kujerar shugaban ma’aikata a sabuwar gwamnatin zababben shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu da za a kafa karshen watan Mayun shekarar na ta 2023.

Gwamna El-Rufai ya musanta rade-raden ne ranar Asabar a jihar Gombe yayin tattaunawa da manema labarai.

Gwamnan ya je jihar ta Gombe ne domin kaddamar da aikin gina gidaje 550 da gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya zai yi.

El-Rufai ya ce hasashen da mutane ke yi maganganu ne kawai na kan titi.

An ambato gwamnan na Kaduna na cewa ya fi mayar da hankali ne kan samar wa Najeriya ci-gaba maimakon kwadayin wani mukami.

Ya kara da cewa ba dole ne sai mutum ya kasance cikin gwamnati ba kafin ya taimaka wajen ci gaban Najeriya, don haka ko baya cikin gwamnati zai dukufa wajen ciyar da ita gaba a cewarsa.

“Ban tattauna da zababben shugaban kasa kan wannan batun ba don haka ba na son jita-jita.

“Na karanta yadda ake ta danganta ni da mukamai daban-daban a wasu jaridu, to amma kun san ni dan Najeriya ne da ya dukufa wajen ciyar da ita gaba” in ji El-Rufai.

Ya kara da cewa ya fi son ya ga kasarsa na ci gaba kuma zai yi dukkan abin da zai yuwu wajen ganin haka.

Gwamnan na Kaduna ya ce idan ya sauka daga mulki a karshen watan Mayu, zai dauki lokaci ya huta wa ransa, amma kuwa zai bayar da shawara idan bukatar hakan ta taso domin ciyar da kasarsa gaba.

Nasir El-Rufai ya sake tabbatar wa ‘yan Najeriya ba za su yi nadamar zaben Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa ba domin kyawawan manufofinsa.

A ranar 29 ga watan Mayu ne Gwamna Nasir El-Rufai zai mika mulki ga sabon zababben gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani wanda dan jam’iyyarsa ta APC ne.

Ya zuwa yanzu zababben shugaban kasar na Najeriya Bola Tinubu bai ambaci sunan kowa da zai yi aiki da shi ba a manya da kananan mukamai da shugaban kasa ke bayarwa bayan ya karbi ragamar mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here