Messi na son tafiya Al Hilal, Raphinha zai bar Barcelona

0
120

Bayanai na nuna cewa Lionel Messi, zai tafi Al Hilal ta Saudiyya, wanda idan har hakan ta kasance dan wasan Najeriya Odion Ighalo, zai bar kungiyar. (Sky Sports)

To amma PSG na son Messin ya tsaya domin sai ta yi masa gwaggwaban tayi na albashi. (Sunday Times)

West Ham na son sayen dan wasan tsakiya na Manchester City da Ingila Kalvin Phillips da dan baya Kyle Walker. (90min)

Dan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes, zai sanya hannu a sabuwar yarjejeniya a Newcastle wadda za ta sa ya zama dan wasan da ya fi karbar albashi mai yawa a tarihin kungiyar. (Football Insider)

Juventus na son karbar aron dan wasan gaba na Ingila Mason Greenwood, daga Manchester United. (Sun)

Liverpool ta kwallafa son dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Mason Mount. (Mail )

Bisa ga dukkan alamu dan wasan tsakiya na Brighton Alexis Mac Allister, wanda ya dauki Kofin Duniya da Argentina, zai koma Liverpool. (Football Insider)

Dan wasan Brazil Raphinha, zai duba yuwuwar barinsa Barcelona a bazaran nan mai zuwa.

Tuni kuma Arsenal ta nuna sha’awarta da tsohjon dan wasan na Leeds wanda Chelsea da Newcastle ma suke so. (Sport – in Spanish)

Watakila Tottenham sai ta biya Bayern Munich fam miliyan 10 kafin ta Julian Nagelsmann ya tafi ya zamar mata sabon kociya. (Sunday Telegraph)

Sai dai kuma kociyan Bayer Leverkusen Xabi Alonso shi ne wanda shugaban Tottenham Daniel Levy ya fi so. (Sunday Mirror)

Manchester City da Arsenal suna son sayen dan wasan tsakiya na AC Milan Ismael Bennacer, dan Algeria. (FootballTransfers)

Har yanzu dan wasan tsakiya na Austria Marcel Sabitzer, zai tattauna makomarsa da kociyan kungiyarsa Bayern Munich, Thomas Tuchel ba.

A yanzu dai Sabitzer yana zaman aro ne a Manchester United. (Sky Germany, daga Manchester Evening News)

Tsohon dan wasan tsakiya na Sifaniya da Barcelona Andres Iniesta, mai shekara zai bar kungiyar Vissel Kobe ta Japan da bazara. (Nikkan Sports )

Kungiyoyin West Ham, Crystal Palace da Leicester na sha’awar dan wasan tsakiya na Bournemouth kuma dan Colombia Jefferson Lerma. (Team Talk)

Manchester City na son tattaunawa a kan sabon kwantiragi da matashin dan wasan tsakiya James McAtee mai shekara 20 bayan da ya taka rawar gani wajen nasarar Sheffield United zuwa Premier a lokacin da yake zaman aro a Bramall Lane. (Mail)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here