Uwar gidan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua, Turai ‘Yar’adua ta bai wa matar shugaban ƙasa mai jiran-gado Remi Tinubu shawara kan yadda za ta fuskanci harkokin ofishin matar shugaban kasa.
A hirarta da BBC Hajiya Turai ta ce matuƙar kina kan muƙamin (First Lady) to sai “kin yi haƙuri, saboda idan mijinki zai tsaya ya yi irin abin da Umaru ya yi, ya hana a yi ba daidai ba shi ma kuma ya ƙi yin ba daidai ba, to ke za a riƙa zargi.
“Ni ma haka na zama, domin mijina ba ya shan giya ba ya neman mata, kuma ba a same shi da cin hanci ba,” in ji Turai.
Ta ƙara da cewa sai laifi ya koma kanta a matsayinta na matar shugaban ƙasa, don haka babu abin da Remi za ta yi sai haƙuri.
“Babu wanda zai bai wa shugaban ƙasa shawarar gaskiya sai matarsa, duk wanda yake zagaye da shi zai gaya masa abin da yake son ji ne kawai.
Turai ta ci gaba da cewa, “Za ta faɗa masa abin da ta ji ana faɗa ba tare da tsoro ba, kuma ta ba shi shawarar ya bincika domin tabbatar da gaskiya.”
Wani abu ne da aka saba da shi a ‘yan shekarun nan, yadda matan shugabannin ƙasa ke taimaka wa mazajensu wajen cimma abin da suke nema yayin mulkinsu.
Ba kuma kawai a Najeriya ne hakan ke faruwa ba, har ma da kasashen duniya daban-daban.
Wasu daga cikin fitattun matan shugabannin ƙasa da suka taka rawar a-zo-a-gani a mulkin mazajensu sun haɗa da, Hillary Clinton matar Shugaban Amurka Bill Clinton da ya yi mulki a ƙarshen shekarun 1990.
Akwai Michelle Obama da Lalla Salma matar Sarkin Morocco da Chantal Biya matar Shugaban Kamaru da Margaret Gakuo Kenyatta matar tsohon Shugaban Kenya, Uhuru Kenyata.
A ranar 29 ga watan Mayun da ake ciki ne za a rantsar da sabon shugaban Najjeriya Bola Ahmed Tinubu.
Ana sa ran mai dakin nasa za ta taka rawar gani a mulkinsa, ganin cewa ita kanta ‘yar siyasa ce, wadda a baya ta taba zama sanata.