Fasinjojin da ke filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja sun shiga cikin firgici a yayin da jirgin Max Air ya yi hadari bayan da tayar jirgin ta fashe ta kuma kama da wuta.
Hausa 24 ta ruwaito cewa jirgin da abin ya shafa ya taso ne daga Yola na jihar Adamawa.
An yi sa’a, Hukumar (ARFFS) da na Yaki da Wuta cikin sauri ta shawo kan alamari al’amarin.
Tsohon shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA), Dokta Mike Ogirima, ya yi bayani kan lamarin, inda ya bayyana cewa tayar jirgin ta fashe ne bayan tashi daga filin jirgin saman Yola.
Ogirima ya ce, “Mun gode wa Allah. Har yanzu muna kan titin jirgi kuma matukin jirgi ya tabbatar mana. Ya kira stairs, yanzu haka muna sauka daga titin jirgin domin a kwashe mu zuwa ginin zauren isowa na filin jirgin.
“Mun yi wa Allah godiya saboda mun shaida yadda aka fiddo taya daga filin jirgin sama na Yola kuma mun shiga taron addu’a. Ban taba sanar da shi a matsayin likitan fida ba don kada a firgita amma mun gode wa Allah.”
Sai dai duk da haka jirgin ya samu zuwa Abuja kafin ya yi hadari, inda tuni jami’an agajin suka je kasa domin kashe gobarar kafin saukar fasinjojin a titin jirgin.
An kwashe fasinjojin daga titin jirgin cikin koshin lafiya, yayin da ita kanta titin jirgin aka rufe na wani dan lokaci har sai an dauke jirgin.
Daga karshe wani jami’in kamfanin ya tabbatar da cewa dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin suna cikin koshin lafiya, yana mai godiya ga Allah da ya tsare su.