‘Yansanda sun damke wani mutum da ya kashe matarsa a Adamawa

0
116

Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa ta cafke wani magidanci mai suna Aminu Abubakar mai shekara 56 bisa laifin kashe matarsa.

Abubakar, mazaunin Lelewaji, a yankin Shagari Phase 2 a Yola, a karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar, an zargin ya yi wa matarsa ​​Nana Fadimatu dukan tsiya wanda ya yi ajalinta har lahira, bayan ya fahimci shirinta na auren wani mutum.

Ana zargin Abubakar da sakin mamaciyar har sau biyu tare da ba ta masauki ba, har zuwa lokacin da za a sasanta auren.

Amma kafin su sasanta, an ce marigayiyar na shirin auren wani mutum, lamarin da ya harzuka Abubakar, inda ya shiga tashin hankali.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, “Wanda ake zargin, Aminu Abubakar, mazaunin Lelewaji, Shagari Phase 2, a karamar hukumar Yola ta Kudu, ya yi wa marigayiya Nana Fadimatu dukan tsiya bayan wata ‘yar rashin jituwa da ta barke tsakaninsu lokacin da ya ji labarin cewa marigayiyar za ta auri wani daban.

“Wanda ake zargin ya fusata ya danne ta a ranar 5/5/2023 da misalin karfe 10 na dare, inda ya buge ta da karfi ta hanyar buga mata wani abu mai kauri sakamakon hakan ta fadi a sume sannan aka sanar da cewa ta mutu.

“’Yansanda sun kama wanda ake zargin ne a hedikwatar ‘yansanda ta Shagari sakamakon rahoton da aka samu daga sabon angon nata, Mahmud Rufa’i na Shagari a karamar hukumar Yola ta Kudu.

“Bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa wanda ake zargin shi ne manajan kamfanin ruwa na Anasam a gidan Jambutu 50 yana da ’ya daya tare da marigayiyar bayan shekaru tara da aurensu.

“Kwamishanan ‘yansanda CP Afolabi Babatola yayin da yake bayyana kaduwarsa ya yaba wa DPO din Shagari bisa kama wanda ake zargin.”

Ya kara da cewa CP din ya umarci jami’an sashen yaki da kisan kai da ke ma’aikatan CID na jihar da su dauki nauyin gudanar da bincike tare da tabbatar da cewa doka ta yi aiki.

Haka zalika ya yi kira ga jama’ar yankin da su rika kai rahoton mutanen da ba su da alaka da su a unguwanninsu ga ‘yansanda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here