Rundunar sojin Najeriya ta yi Allah wadai da wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta wanda ya nuna wasu mutane sanye da kakin soji suna cin zarafin farar hula.
A bidiyon, an ga wasu farar hula suna rarrafe a cikin kwata inda wasu mutane sanye da kayan soji suke dukansu da bulala a wani otel da ke jihar Kaduna.
Sanarwar da sojojin suka fitar ranar Lahadi dauke da sa hannun daraktan hulda da jama’a na rundunar Onyema Nwachukwu, ta ce abin da suka yi ya saba wa ka’idar aiki da kwarewa da sadaukar da kai domin kare bil adama wadanda aka san sojojin Najeriya da su.
“Rundunar sojin Najeriya ta bayar da umarnin gudanar da bincike nan take kan murya da kuma bidiyon domin gano gaskiyarsa, da kuma gano wadanda ake zargin.
“Za a hukunta mutanen da suka aikata mummunan aiki sanye da kakin soji idan bincike ya gano cewa sojoji ne kamar yadda dokar sojojin Najeriya ta tanada,” in ji sanarwar.
Ana yawan samun bidiyo yana karade shafukan sada zumunta kan cin zarafin da jami’an tsaro ke yi wa farar hula a Nijeriya.
Ko a watan jiya sai da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta rage wa wasu jami’anta girma sakamakon samunsu da laifin cin zarafin farar hula.
Haka ma a bara an ga yadda hukumar ta ‘yan sanda ta sallami wani jami’inta a Jihar Delta da ke kudancin Najeriya mai suna Ubi Ebri kan zargin kashe wani matashi mai shekara 26.