Home Labarai Labaran Duniya Wata nakiya da aka binne ta kashe sojojin Nijar 7

Wata nakiya da aka binne ta kashe sojojin Nijar 7

0
88

Akalla Sojoji Nijar 7 ne suka gamu da ajalinsu bayan da motarsu ta taka wata nakiya da aka binne a yankin Tillaberi da ke yammacin jamhuriyar kasar.

Wata sanarwa da rundunar sojin Nijar ta fitar na nuna cewa motar na dauke da kayayyakin da ake isar wa sojoji na mako-mako ne kafin ta afkawa nakiyar da aka binne da sanyin safiyar a kusa da kauyen Samira.

Kauyen da ke iyakar Nijar da Burkina Faso a kudu maso yammacin kasar, shine yanki daya tilp da gwamnati ke hakar zinare tun a shekara ta 2004.

Wannan harin dai shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren da aka kai wa sojojin Nijar.

Kasar dake yankin Sahel na fama da hare-haren daga masu ikirarin jihadi dake da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS, sai kuma a yankin Kudu maso Yamma kuma take fama da mayakan Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp