Ƴan sanda sun fara kamen karuwai a cikin garin Katsina

0
163

Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta kamo wasu karuwai su hudu a bakin wani gidan badala dake cikin garin Katsina.

Kakakin rundunar, CSP Gambo Isah ne ya gabatar da su a gaban ƴan jarida ranar Litinin ɗin da ta gabata a hedikwatar yan sandan dake cikin garin Katsina.

Wadanda aka kamo din sun hada da Fati Jafar wadda aka fi sani da Yar Fulani, Bushira Hamisu, da Jamila da kuma Fatima.

Da ake yi masu tambayi, matan sun bayyana cewa kaddara ce ta fito da su daga gidajen iyayen su kuma suna da niyyar komawa nan ba da dadewa ba.

Sai dai da aka tambaye su ko me suke yi a wurin sadda aka kamo su, dukkan su sun bayyana cewa sana’a suke yi a wurin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here