An kafa dokar hana tsadar aure a jihar Sokoto

0
126

Majalisar Jihar Sokoto da ke Najeriya ta sanya hannu kan wani kudirin dokar da ke sanya ido kan tsada da almubazzarancin da jama’a ke yi a bikin aure a jihar.

Kudirin wanda Alhaji Abubakar Shehu na jam’iyyar APC da Faruk Balle na Jam’iyyar PDP suka gabatar, sai da aka fara gabatar da shi ga Kwamitin Kula da Al’amurran Addini a majalisar.

Shehu wanda shi ne shugaban kwamitin, ya gabatar da rahotonsu a wani zaman farko na ‘yan majalisar kuma daukacinsu suka amince ya zama doka.

Kudirin dokar na bukatar sanya ido kan almubazzarancin kudi da ake yi a yayin bikin aure da taron suna da kaciya da sauran bukukuwa a sassan jihar.

Bayan wata muhawara a zaman na farko da mataimakin shugaban majalisar ya jagoranta, Alhaji Abubakar Magaji, kudirin dokar ya samu amincewar ‘yan majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here