An kama wani kwarto da ke shiga gidan matan aure yana zina da su a Daura

0
136

Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta samu nasarar cafke wani matashi mai suna Buhari Dahiru da ya ce shekarun sa 20 da haihuwa dake kutsawa gidajen matan aure yana lalata da su a garin Daura.

Mai magana da yawan rundunar Ƴan sandan ne na jihar Katsina, CSP Gambo Isah ya bayyana mai laifin gaban yan jarida ranar Litinin a hedikwatar yan sandan dake cikin garin Katsina.

A cewar sa, mai laifin ya aikata alfashar sau biyu kafin dubun sa ta cika lokacin da yake ƙoƙarin aikata na uku.

Da yake bayar da labarin yadda yake aikata laifin, Buhari Ɗahiru ya ce yana zuwa ne gidajen matan auren lokacin da ya tabbatar da cewa mijin su ba ya gida sai ya kwankwaso masu ya ce mai gidan ne ya aiko shi da sako.

Buhari ya cigaba da cewa idan matan suka bude gidan domin su karɓi sakon su sai ya kutsa kai ciki ya kuma tsoratar da matan ta hanyar fiddo wuka ya nuna masu kafin daga bisani ya yi lalata da su.

Sai dai kamar yadda CSP Gambo Isah ya bayyana, dubun sa ta cika ne lokacin da yayi kokarin yin lalata da wata matar auren amma sai ta kira mijin ta wanda ya dawo gida da sauri ya kuma tattara jama’a suka kama shi.

CSP Gambo Isah ya ce mata biyun da ya yi anfani da su kafin a kama shi duk suna da juna biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here