Jirgin ruwa ya nutse da mutum 20 a Sakkwato

0
128

Jirgin ruwa ya nutse da mutum 20 da suka tashi daga kauyen Dundeji zuwa Kambama a Karamar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato.

Mutanen sun bar gidajensu a ranar Talata da misalin 12 na rana domin tafiya samo itacen girki, sai jirgin ya nutse da su gaba daya.

Masu aikin ceto sun tsamo mutum 15 ana neman biyar a yanzu haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here