Kotun koli ta tabbatar da kawun Davido a kujerar gwamnan Osun

0
121

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a 2022.

Kotun Kolin ta kuma yi watsi da karar Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a zaben Gwamnanda tsohon Gwamna, Adegboega Oetola na Jam’iyyar APC ya shigar na kalubalantar cancantar Adeleke na tsayawa takara a zaben.

Ta kuma caccaki Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Osun da ta ki amfani da hukuncinta na farko kan halaccin taakarar Adeleke.

Adekele kawu ne ga fitaccen mawakin Najeriya, Davido, wanda kuma ya yi a fadi-tashi tun lokacin yakin neman zaben kawun nasa.

Ko a makon jiya mawakin ya addu’ar samun nasara  ga kawun nasa, wanda wasu ke wa lakabi da gwamnan mai rawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here